Search
Close this search box.

Hizbullah Ta Kai Harin Makamai Masu Linzami Akan Sansanin Sojan HKI A Yankin Jalil

A mayar da martani da hare-haren wuce gona da iri na HKI akan kasar Lebanon, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kai wa sansanin sojan ‘yan

A mayar da martani da hare-haren wuce gona da iri na HKI akan kasar Lebanon, kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ta kai wa sansanin sojan ‘yan mamaya dake yankin Jalil hari da makamai masu linzami.

Bugu da kari dakarun na kungiyar Hizbullah sun kai wani harin da makamai masu linzami akan sansanin ‘yan sahayoniya na Kafar-Kala.

A sansanin ‘yan share wuri zauna na kiryat Shmona an rika jin jiniyar gargadi tana kadawa.

Tun daga farkon shelanta yaki akan yankin Gaza ne dai kungiyar ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta shiga cikin masu taya Falasdinawa fada akan HKI.

Kungiyar ta Hizbullah tana kai hare-hare akan sansanonin sojan mamaya da kuma cibiyoyinsu na leken asiri.

Da safiyar yau Laraba ma dai kungiyar ta Hizbullah ta sanar da kai hari akan babbar cibiyar sojan ‘yan mamaya ta “ Branet’ ta hanyar amfani da makamai masu linzami samfurin | Burkan” wanda kuma ya yi barna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments