Search
Close this search box.

Hizbullah Ta Cilla Makamai Masu Linzami Kan Tuddan Golan Na Kasar Siriya Wanda Aka Mamaye

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tuddan Golan na kasar Siriya da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tuddan Golan na kasar Siriya da aka mamaye.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto bayanan kungiyar Hizbullah a safiyar yau laraba yana cewa, dakarun kungiyar sun cilla makamai masu linzami har 30 a safiyar yau Laraba, sannan a jiya ma sun cilla irinsu a kan yankin a kan cibiyoyin tsaro da leken asiri na HKI.

A cikin wani faifen bidiyo wanda kungiyar ta saka a shafukan yanar gizo, sun nuna yadda makaman suka fada kan matsugunan yahudawa da ake kira ‘Katzirin’.

Har’ila yau labarin ya kammala da cewa dakarun Hizbullah sun cilla makamai har guda 60 a kan sansanonin sojojin HKI a yankin tuddan Golan a cikin kwanaki biyu da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments