Hizbullah Ta Aike Da Jirgi Mara Matuki Wanda Ya Tattaro Bayanai Kan Wuraren Sojin Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da  bidiyo na wani jirgi mara matuki da ta aike, wanda ya ta tattaro bayanai kan wasu

Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta fitar da  bidiyo na wani jirgi mara matuki da ta aike, wanda ya ta tattaro bayanai kan wasu muhimman wurare na sojin Isra’ila,a a cikin yankuna Falastinawa da ta mamaye a shekara ta 1948, da suka hada da tashar ruwa da ta jiragen sama a birnin Haifa.

Kungiyar ta nuna hotuna na tsawon minti tara, daga cikin har da wurare na soji da kuma wurare ajiye makamai, gami da makaman kariya na Isra’ila.

Baya ga haka kuma an nuna hotunan bidiyo da jirgin ya dauka na tashar jiragen ruwa ta Haifa, da jiragen da suke wurin na soji ad abubuwan da suke da su, da kuma cikakkun sunayensu.

Sannan kuma an nuna filayen jiragen sama na yaki an Isra’ila da jiragen da suke wurin da runbunan ajiye makamai a cikin filayen jiragen, da sunayensu baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments