Hizbullah: Amurka ِDa Isra’ila Ba za Su Iya Yin Nasarar Akanmu ba.

Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat

Rahotanni sun bayyana cewa shakih Naim Qassim babban sakatare janar din hizbullah na kasar labanon ya bayyana a jiya Alhamis a gaban mambobin kungiyar Kashafat Al-Mahadi cewa Amerika da Isra’ila ba za su iya yin galaba akan hizbullah ba,

Babban hadafin kafa wannan kungiyar shi ne kokarin wayar da kan yara matasa yan shekara 6 zuwa 18 muhimman alamuran addini, adaidai lokacin da gwamntin sahyuniya take ta kokari wajen yada akidar sahyuniyanci tsakanin yara matasa, kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen yada akidar gwagwarmaya ga matasa masu tasowa inda yanzu haka tana da mambobin fiye da 100,000.

Shaikh Naim Qaseem ya bayyana muhimmancin wannan kungiyar kuma ya bayyana cewa samuwar wadannan matasa zai kara taimakawa wajen tunkarar dukkan kalubalen dake gabanta  ,kuma Allah zai sanya tutarsu ta ci gaba da kasancewa a Sama.

Daga karshe ya nuna cewa kashafa Imam Mahdi wata fitila ce ga matasa masu tasowa zuwa ga kyawawan halaye da kuma jajircewa wajen  neman ilimi, don haka da goyon bayanku zamu ci ga ba da samun nasararoi har zuwa samun zaman lafiya da yanci ga dukkan alumma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted