Hezbollah ta harba makaman roka a kan yankin masana’antu na Isra’ila a Haifa

Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa ta harba makaman roka a kan yankin masana’antu na Isra’ila da ke kudancin Haifa, a wani mataki na ramuwar

Kungiyar Hizbullah ta sanar da cewa ta harba makaman roka a kan yankin masana’antu na Isra’ila da ke kudancin Haifa, a wani mataki na ramuwar gayya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Kungiyar Hizbullah ta kuma bayar da rahoton hare-hare kan sansanin Miron da ke gudanar da ayyukan jiragen sama, da kuma sansanin Ma’aleh Golani, cibiyar bayar da umarni ta rundunar Hermon Brigade 810, inda ta yi amfani da makaman roka wajen kai harin.

Ban da wannan kuma, kungiyar Hizbullah ta kai hari kan makaman atilare na sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a matsugunan Neot Mordechai ta hanyar yin amfani jiragen sama marasa matuka, inda suka yi nasarar kai hari kan wuraren da suka nufa.

Haka nan kuma kungiyar ta bayyana cewa ta harba makaman roka kan dandazon  sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a wajen garin Maroun al-Ras na kasar Lebanon, da kuma wurare daban-daban da na arewacin Falastinu da ke karkashin mamayar Isra’ila, da suka hada da Kiryat Shmona, Nahariyya, sansanin sojan Dovif, Ramtha, Yiftah da kuma yankin Margaliot.

Kungiyar Hizbullah ta kuma nuna hotunan bidiyo da aka dauka a lokacin da mayakanta suke harba rokoki a wasu matsugunan yahudawa ‘yan share wuri zauna.

Kafafen yada labaran kasar Labanon sun ce an kashe daruruwan sojojin Isra’ila tun lokacin da suka kaddamar da farmaki a kudancin Lebanon a farkon watan Oktoba.

Kafafen yada labaran Isra’ila kuma sun amince da karuwar adadin wadanda suka halaka daga cikin sojojin mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments