Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; daya daga cikin sojojinsu ya halaka sanadin harin da kungiyar Hizbullah ta kai da makami mai huda motoci masu silke.
Kafafen watsa labarun na HKI sun ambaci cewa; Hizbullah ta fadada yankunan datake kai wa hari a Isra’ila, da hakan ya takawa sojojin HKI birki na kasa sanin abinda za su yi.
A can arewacin Palasdinu dake karkashin mamaya, yankunan da ‘yan share wuri zauna su ka kauracewa sun kai 10% na dukkanin Isra’ila kamar yadda kafafen watsa labarun su ka ambata.
Wasu kafafen watsa labarun na HKI sun bayyana cewa;sojojin sahayoniya sun zama matsarota a gaban kungiyar Hizbullah.”
A gefe daya jirgin yakin HKI maras matuki ya kai wasu hare-hare a kudancin Lebanon,musamman a yankin Zabqin da Yatir
Tashar talbiji din ‘almayadin’ ta bayyana cewa; An ji karar jirgin maras matuki da ya ratsa ta samaniyar yankin, amma dai babu hari a cikin yankin.