Search
Close this search box.

Harin Isra’ila A Nuseirat, Na Daya Daga Cikin Mafi Muni A Tarihin Yakin Gaza

Kasashen duniya na ci gaba da yin Allaha-wadai da farmakin da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat dake tsakiyar Gaza.  

Kasashen duniya na ci gaba da yin Allaha-wadai da farmakin da Isra’ila ta kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat dake tsakiyar Gaza.  

Ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce Isra’ila ta kashe Faladinawa fararen hula 274, ciki harda kananan yara, bayan luguden wuta da ta yiwa sansanin mai matukar cunkoson jama’a domin ceto Isra’ilawa hudu da aka yi garkuwa da su.

A wadannan alkaluman da hukumar lafiya a Gazan ta fitar, harin zai zamo daga cikin mafiya muni a tarihin yakin.

A ranar Asabar ne dakarun Isra’ila suka kai hare-haren sama da kuma yin musayar wuta da mayakan Hamas ta kasa a sansanin na Nuseirat.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce mutane akalla 100 suka mutu a yayin fadan.

Iran, a nata bangare ta caccaki shurin kasashen Duniya akan munanen kisan da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa a Gaza, musamman na baya baya nan a sansanin Nuseirat.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Kan’ani ya ce kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa, musamman mata da kananan yara a sansanin al-Nuseirat, ya samo asali ne sakamakon gazawar da kasashen duniya suka yi wajen tunkarar zaluncin da gwamnatin kasar ta yi a Gaza cikin watanni 8 da suka gabata.

Ita ma Turkiyya ta yi Allah wadai da harin na Nuseirat,  inda Ma’aikatar harkokin wajen kasar cikin wata sanarwa ta ce: “tana matukar takaicin harin da Isra’ila ta kai kan sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza, wanda ya kashe daruruwan Falasdinawa.

Inda ta bayyana harin a matsayin “babban laifi” wannan ya bi sahun jerin laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a Gaza, inji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments