Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kashe Fursunoninsu Da Aka Yi Garkuwa Da su A Gaza

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Yawancin fursunonin yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su a arewacin Gaza sun bace a

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Yawancin fursunonin yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su a arewacin Gaza sun bace a halin yanzu

Wata majiya mai karfi a rundunar Izzuddeen Al-Qassam ta bayyana cewa: A halin yanzu mafi yawan fursunonin yahudawan sahayoniyya da ake tsare da su yankin arewacin Gaza sun bace saboda hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan yankunan Falasdinawa.

Jagoran dakarun Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, ya kara da cewa: Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun sha yin gargadi kan mummunan sakamakon hare-haren wuce gona da iri kan yankunan Falasdinawa da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa Gaza.

Jagoran na Qassam ya soki fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da sojojin mamaya, yana mai cewa “sun dage kan guje wa batun gudanar da musayar fursunoni ta kyakkyawar hanyar da ta dace,” yana mai jaddada cewa Dakarun Qassam sun sake dorawa gwamnatin mamayar Isra’ila da sojojinta cikakken alhakin rayuwa da makomar fursunonin su.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments