Jiragen Yakin HKI Sun kai hare-hare kan wasu muhimman wurare a kudancin kasar Lebanon, wanda hakan keta yarjeniyar tsagaita wuta a tsakanin kasashen biyu.
Kamafanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kusa da kogin Litan, Yohmor Al-shaqif da kuma Zoutr Al-sharqiyya, da kuma Deir Siryan, zibqin da Yater. Babu rahoto kan wadanda suka ji rauni ko suka rasa rayukansu.
Gwamnatin HKI ta bayyana cewa ta kai hari ne kan rumbunann ajiyar makamai na kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon.
Duk ntare da tsagaita wuta tsakanin Hizbullah da kuma HKI a ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, bayan watanni 14 da fafatawa, sojojin HKI sun ci gaba da kai hare-hare a cikin kasar Lebanin suna kashesu suna lalata makamasu suna kuma rurrusa gidajensu.
Gwamnatin kasar Lebanon ta shigar da kara a gaban MDD kan kan keta hurumin da HKI yiwa yarjeniyar tsagaita wuta a kasar ta Lebanon amma babu wani abu da ta iya in banda yin allawadai da shi. A ranar 27 ga watan Jenerun da ya gabata, gwamnatin kasar Lebanon ta amince ta tsawaita kasancewar sojojin HKI a kudancin kasar Lebanon.