Hare-haren Hizbullahu Na Safiyar Yau Talata Sun Rusa Gidaje Da Tashin Gobara A Sansanin Nahariya

‘Yan Sandan HKI a matsaugunin ‘yan share wuri zauna na Nahariya sun ambaci cewa makamai masu linzami da kungiyar Hizbullah ta harbo daga Lebanon sun 

‘Yan Sandan HKI a matsaugunin ‘yan share wuri zauna na Nahariya sun ambaci cewa makamai masu linzami da kungiyar Hizbullah ta harbo daga Lebanon sun  fada akan gidaje da motoci da su ka kone da kuma tashin gobara a yankin.

Ita kuwa hukumar agaji ta ‘yan sahayoniyar  a matsugunin ‘yan sahayoniyar ta sanar da cewa, mutane biyu ne su ka jikkata sanadiyyar faduwar makamai masu linzami da aka harbo daga kasar Lebanon.

Su kuwa sojojin HKI sun ce, an harba makamai masu linzami 10 daga Lebanon zuwa yankin Jelil-Garbi, tare da haddasa barna ta dukiya.

A gefe daya, wata kafar watsa labarun HKI ta ambato jami’in da yake kula da Nahariya yana kiran mutane da kar su fita daga gidajensu sai idan har yaza dole daga nan har zuwa sa’oi 48 masu zuwa..

Majiyar tsaro ta yi hasashen cewa daga nan zuwa sa’oi 24  “Isra’ila” za ta fuskanci ruwan makamai masu linzami daga Lebanon.”

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments