Hamas : ‘Yan Mamaya Na Aikata Laifuka Tare Da Cikakken Goyan Bayan Amurka

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta nuna matukar nadamar ta akan yadda Isra’ila ke ci gaba da mamayar da ta ke, bisa cikakken goyan bayan

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta nuna matukar nadamar ta akan yadda Isra’ila ke ci gaba da mamayar da ta ke, bisa cikakken goyan bayan Amurka da kuma manyan kasashen yammacin Turai.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Isra’ila ta na ci gaba da aikata laifuka da kisan kiyashi kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza a yayian da duniya ta yi gum da bakinta kan laifukan da Isra’ila ke ci gaba da aikatawa.

Na baya baya nan shi ne ta’adin da Isra’ilar ta aikata a yankin Zawaida, a tsakiyar Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar shahidai da dama daga gida daya, wadanda akasarinsu yara ne.

Rahotanni sun ce akalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin na Isra’ila a tsakiyar Zirin.

Kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Asabar cewa : “Wadannan cin zarafi da laifuffukan da ake yi wa Falasdinawa, da suka hada da yara, mata da tsofaffi, suna ci gaba a idon duniya tare da cikakken goyon bayan gwamnatin Amurka da manyan kasashen duniya.

Kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da Majalisar Dinkin Duniya da rassanta da su daina shirun da suke da shi, su kuma dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na kare Falasdinawa, da kawo karshen wadannan munanan laifukan da ake yi wa al’ummar Falastinu da kuma dorawa ‘yan sahyoniya laifukan yaki da suka aikata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments