Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya .
Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu.
Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa yankin gaza, tana mai jaddada wajibci sharia’ a matsayinta na wadda ta mamaye yankin ta tabbatar da an shigar da dukkan kayan agaji zuwa yankin domin mikawa falasdinawa, kana kuma tayi wasti da zargin da isra’ila ta yin a cewa hukumar UNRWA tana alaka da kungiyar Hamas.
Hukumcin da kotun ya yanke ya haramta amfani da yunwa a matsayin wani makamin yaki, kuma yace mamaya da kashe falasdinawa da gangan wani nau’I ne na kisan kare dangi.