Hamas Ta yi Watsi Da Amincewa Da Kudurin Amurka Da Kwamitin Tsaro Ya yi Kan Gaza

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da daftarin kuduri da kasar Amurka ta gabatar mata na kafa sansanin sojojin kasa da kasa a yankin Gaza.

An amince da kudurin ne a jiya litinin inda aka amince da shirin na Donald Trump kan Gaza kuma ta bada umarnin kirkiro dakarun kasa da kasa na hadin guiwa da zai hada da mafiyawancin daga kasashen musulmi da zai kunshi  kasashen Masar, Indonesia, da kuma kasar Azarbaijan,

Kungiyar Hamas ta yi watsi da wannan kuduri da zai kunshi dakarun kasada kasa domin baya wakiltar hakkokin falasdinawa kuma an yi shi ne domin kwabe dammarar dakarun gwagwarmayar neman yancin falasdinu.

Haka zalika ta kara da cewa kudurin bai kunshi bukatun siyasa da taimakon jinkai da kuma hakkokin alummar  falasdinu ba, don haka cewa duk wani sojan kasa da kasa da zaa aika zuwa iyakar gaza ne kawai, domin sa ido kan yadda ake aiki da dakatar da bude wuta karkashin kulawar majalisar dinkin duniya.

Sai dai kasashen rasha da china sun kada kuriar nuna rashin amincewa da kudurin na Amurka .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments