Search
Close this search box.

Hamas Ta Musanta Cewa Ta Maida Makarantar Tabi’in A Gaza A Matsayin Cibiyar Yakar Sojojin HKI

Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin zirin Gaza ta musanta zargin HKI na cewa ta maida makarantar Tabi’in na Gaza ya zama cibiyar yakar

Kungiyar Hamas wacce take iko da yankin zirin Gaza ta musanta zargin HKI na cewa ta maida makarantar Tabi’in na Gaza ya zama cibiyar yakar sojojin Haramtacciyar kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan  Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a wani bayani da ta fitar a safiyar yau Lahadi ta kuma kara da cewa gwamnatin yahudawan ta yi wannan zargin ne don ta halattawa kanta kisan kiyashin da ta aikata a jiya da safe a makarantar, inda a lokaci guda mutane fiye da 150 suka rasa rayukansu.

Banda haka bayanin kungiyar ya kara da cewa babu wani daga cikin dakarun izzudden Qassam, wato mayakan Hamas da ya rasa ransa a hare haren, sabanin rahoton HKI na cewa ta kashe dakarun Hamasa 19 a hare haren makarantar Tabi’in. Rahoton ya kammala da cewa gwamnatin HKI ta kirkiro wannan kariyar ce don ta kare kanta daga allawadai da aka yi mata a duk fadin duniya saboda kisan kiyashin na makarantar Tabi’in da ke unguwar Al-Darraj na birnin Gaza.

A sannin safiyar jiya Asabar ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan makarantar Tabi’in da ke Gaza a dai dai lokacinda Falasdinawa yan gudun hijira wadanda suke samun mafaka a makarantar suke sallar asubaha.

Kasashen duniya da kungiyoyi daban daban sun yi allawadai da kissan kiyashin na  jiya, sun kuma bukaci HKI ta kawo karshen yaki a Gaza.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa batun yerjeniyar tsagaita bude wutan da HKI take magana a kanta a cikinn kwanakin nan karya ce bayan wannan kissan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments