Kungiyar Hamas wacce take fafatawa da sojojin HKI a Gaza kimani shekara guda da ta gabata, ta bayyana cewa gwamnatin HKI tana amfani da yan gudun hijira daga kasashen Afirka don yakar kungiyar Hamas a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin HKI tana tilastawa yan gudun hijira mafi yawansu daga kasashen Amurka shiga yaki a gaza bayan samun horaswa kadan. Ta kuma yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bail’adama a kasashen duniya su san da wannan su kuma dauki matakan da suka dace kan shuwagabannin HKI.
Kungiyar ta kara da cewa shuwagabannin HKI suna aikata laifufuka kan wasu laifukan da suka aikata, tare da tilastawa yan gudun hijira shiga yaki a Gaza. Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewa gwamnatin HKI a halin yanzu tana neman yan gudun hijira daga kasashen Afirka wadanda zata basu visar shiga kasar don yaki a gaza, saboda karancin sojojin da take fama da shi. Da kuma kin shiga yaki wanda matasa yahudawa suka yi.