Hamas Ta Fitar Da Bayani Akan Zaben Sabon Shugabanta

A wani bayani da kungiyar Hamas ta fitar na juyayin shahadar Isma’ila Haniyyah ta bayyana cewa ba al’ummar Falaasdinu ce kadai ta yi rashinsa ba,

A wani bayani da kungiyar Hamas ta fitar na juyayin shahadar Isma’ila Haniyyah ta bayyana cewa ba al’ummar Falaasdinu ce kadai ta yi rashinsa ba, dukkanin al’ummar Larabawa da musulmi suna kewayarsa. Haka nan kuma dukkanin ma’abota ‘yanci na duniya,domin su ma sun yi rashinsa,  babban dalili shi ne yadda dukkanin duniya ta nuna damuwa akan abinda ya faru.

Kungiyar ta Hamas ta sanar da cewa; Tun sa’o’in farko na shahadar Isma’ila Haniyyah,majalisar shawarar kasar ta yi taro inda ta tattauna abinda da ya faru sannan kuma da cimma matsaya akan wasu manufofi.

Bugu da kari, kungiyar t ace, shahadar dan’uwa Isma’iliyyah Haniyyah ba abinda zai karawa kungiyar sai karfi da tsayin daka.

Har ila yau, kungiyar ta “Hamas” ta ce, tana da cibiyoyi masu karfi, wannan kuwa wani abu ne da yake tabbatacce a cikinta.

Wani bangare na bayanin kungiyar ta “Hamas” ya kunshi cewa: Muna  tabbatarwa al’umma cewa; Kungiyar tana cigaba da gudanar da ayyukanta, ba tare da wani cikas ba.

Share

3 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments