Hamas ta bukaci Trump ya dauki darasi daga kuskuren Biden, ya kawo karshen goyon bayan Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce dole ne sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump ta dauki darasi daga kura-kurai na Joe Biden, sannan ta

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce dole ne sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump ta dauki darasi daga kura-kurai na Joe Biden, sannan ta yi aiki da gaske wajen dakile kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinu.

A cikin jawabinsa na nasara, zababben shugaban ya yi ikirarin cewa “zai kawo karshen yake-yake.”

Trump dai ya sha ikirarin cewa da a ce shi ne shugaban kasa, da tun farko Isra’ila ba ta fara yakin kisan kare dangi a Gaza ba.

A cikin sanarwar da Hamas ta fitar yau Laraba ta ce matsayinta ga gwamnatin Amurka mai zuwa zai dogara ne kan “halayenta na zahiri ga al’ummar Falasdinu.”

“Dole neTraump  ya yi aiki da gaske don dakatar da yakin kisan kiyashi da cin zarafi kan al’ummar Falasdinawa a zirin Gaza da yammacin kogin Jordan.”

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta bukaci Trump da ya kawo karshen yakin da Isra’ila ke yi a Lebanon, da “dakatar da bayar da tallafin soji ga yahudawan sahyoniyawan, da kuma amincewa da hakki na mutanenmu.”

Bassem Naim, wani mamba a ofishin siyasa na Hamas ya ce “Dole ne a kawo karshen wannan goyon bayan yahudawan sahyoniya ido a rufe.

Ya ce al’ummar Palastinu “ba za su amince da duk wata hanyar da za ta tauye hakkinsu na ‘yanci, yancin kai, da kafa kasarsu ta Falasdinu mai cin gashin kanta tare da Kudus (al-Quds) a matsayin babban birninta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments