Abu Ubaida kakakn dakarun Ezzuddeen Al-Qassam reshen soje na kungiyar Hamasa ya bayyana cewa dakarunsa zasu ci gaba da Yakar sojojin yahudawa har zuwa korarsu daga yankin zirin Gaza.
Abu Ubaida ya kara nda cewa, dakarun Hamas suna a madaka ga sojojin HKI babu jada baya babu janyewa daga matsayinsu.
Kafin haka dai a jiya Jumma’a dakarun na Hamas tare da hadin guiwa da na Saraya Qudus sun aiwatar da wani shiri ko tarko kan sojojin yahudawan wanda ya sami nasara halaka sojojin yahudawa da dam.
Majiyar yahudawan sun tabbatar da aukuwar hare-haren na Khan Yunus dake kudancin Gaza, wanda kuma ya halaka yahufawa da dama.,
Abu ubaida ya kammala da cewa aikin soje da suka yi a Khan Yunus da Jabali yak aiga halakar sojojin yahudawa 5 da kuma jikatar wasu. Ya ce sojojin Hamas sun sake farkawa don haka a jiya Jumma’a suka aikata ayukan soje masu yawa a gaza.