Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.”
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne.
“Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.”
Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da Falasdinawa sama da miliyan biyu ke fama da su, kuma yana nuna yiwuwar fuskantar yunwa a Gaza.
“hana shigar da abinci, magunguna, man fetur, da hanyoyin agaji na yau da kullun ya haifar da tashin gwauron zabin abinci da kuma tsananin karancin magunguna, lamarin da ya ta’azzara matsalar jin kai a Gaza.”
Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani da su matsa wa gwamnatin kasar lamba wajen “cika alkawurran da ta dauka” a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta.