Gwamnatin Natanyahu Ta Rusa Majalisar Ministocin HKI Bayan Ficewar Wasu Manya Manyan Ministoci

Fraiministan HKI Benyamin Natanyahu ya bada sanarwan rusa  majalisar ministocin gwamnatinsa bayan ficewar wasu daga cikin manya manyan ministocin. Tashar talabijin ta Presstv a nan

Fraiministan HKI Benyamin Natanyahu ya bada sanarwan rusa  majalisar ministocin gwamnatinsa bayan ficewar wasu daga cikin manya manyan ministocin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majayar gwamnatin HKI tana fadar haka a yau Litinin ta kuma kara da  cewa, a makon day a gabata ne daya daga cikin ministocin Benny Ganz ya sauka daga mukaminsa tare da zargin Natanyahu da rashin tsari a yakin da yake fafatawa a gaza, da kuma rashin wani shiri na bayan yaki a Gaza.

Har’ila yau Gadi Eisenkot ya ajiye mukaminsa a makon day a gabata shima, saboda wasu dalilai, wadanda suka shafi yakin da gwamnatin Natanyahu take fafatawa a Gaza.

Ya zuwa yanzu dai sojojin Natanyahu sun kashe Falasdinawa kimani dubu 38 sannan wasu fiye da 86 sun ji rauni, mafi yawansu mata da yara.

Dama an dade ana jirin lokacinda frai ministan zai rusa gwamnatinsa nasa, saboda matsalolin da yake fuskanta a yanbkin watannin kimani 8 da sojojinsa suka yi suna fafatawa da Falasdinawa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments