Gwamnatin Kasar Jamus Ta Ce Zata Ci Gaba Ta Tallafawa HKI Da Makamai Duk Tare Da Adawar Jam’iyun Adawa Kasar

Shugaban kasar Jamus Chancellor Olaf Scholz ya ce gwamnatin kasarsa zata ci gaba da tallafawa HKI da makamai duk tare da kin hakan wanda jam’iyyun

Shugaban kasar Jamus Chancellor Olaf Scholz ya ce gwamnatin kasarsa zata ci gaba da tallafawa HKI da makamai duk tare da kin hakan wanda jam’iyyun adawa na kasar da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama suke yi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wazirin kasar ta jamus yana fadar haka a yau Jumma’a a wani taron yan jarida da ya kira a birnin Berlin babban birnin kasar.

Olaf Scholz ya kara da cewa: mun sha bawa HKI makamai kuma bamu ce zamu dakatar ba, don haka zamu ci gaba da bata makamai.

A cikin watan Afrilun da ya gabata ne gwamnatin kasar Nicaragua ta shigar da kara a gaban kotun kasa ta kasa ta ICJ inda ta bukaci kotun ta bada umurni ga kasashen da suke tallafawa HKI da makamai a yakin kissan kare danginda take yi a Gaza, musamman kasar Jamus.

Duk da cewa kotun ta ki ta yi hakan, amma kungiyoyin kare hakkin bil’adama da yan siyasa wadanda suke adawa da HKI kan abinda take aikatawa a gaza duk sun ci gaba da nuna rashin amincewarsu da tallafawa HK da makamai, saboda hakan tallafawa masu aikata laifukan yaki ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments