Amurka tana shirin tura jiragen ruwa na yaki da manyan jirage yankin Gabas ta Tsakiya bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi a Iran da Lebanon, kamar yadda majiyoyin tsaron Amuka suka tabbatar.
Haka nan kuma Amurka ta aika da karin tawaga ta jiragen sama na yaƙi da na’urorin kakkaɓo makamai masu linzami, sakamakon yadda Amurka ke daukar wadannan matakai a matsayin tunkarar barazanar da Iran da ƙawayenta suka yi kan yin martani bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kwana biyu da suka wuce a Tehran da kuma kisan da ta yi wa babban kwamandan Hezbollah a Beirut a yayin da take ci gaba da aiwatar da kisan ƙare-dangi a Gaza.
Sakataren tsaron Amurka ya shaida wa ministan tsaron Isra’ila ƙarin matakan da ma’aikatar tsaro take ɗauka da suka haɗa da sauye-sauyen da za su tabbatar da tsaron Isra’ila,” in ji kakakin Pentagon Sabrina Singh a yayin da take bayar da sanarwa ga manema labarai.
Haka nan kuma ya tabbatar wa minista Gallant da Shugaba Joe Biden da kuma Firaminista Benjamin Netanyahu cewa za mu tura ƙarin matakan tsaro domin kare yankin domin tabbatar da tsaron Isra’ila da kuma bata kariya.