Gwamantin Falasdinu: Ba Za A Sami Zaman Lafiya Ba Sai An Kafa Wa Falasdinawa Gwamnati

Gwamnatin kwarya-kwaryar Falasdinawa ta sanar da cewa; Babu wanda zai sami aminci da zaman lafiya ba tare da an kafa wa Falasdinawa gwamnati ba. Jawabin

Gwamnatin kwarya-kwaryar Falasdinawa ta sanar da cewa; Babu wanda zai sami aminci da zaman lafiya ba tare da an kafa wa Falasdinawa gwamnati ba.

Jawabin na gwamnatin kwarya-kwaryar Falasdinawa ya zo ne a matsayin mayar da martani ga wani dan majalisar HKI wanda ya yi watsi da batun kafawa Falasdinawa gwamnati.

Kakakin gwamnatin kwarya-kwaryar Falasdinawa Nabil Abu Radinah,shi ne wanda ya mayar da martanin ga dan sahayoniyar da ya yi watsi da batun kafa gwamnatin  Falasdinu kamar yadda dokokin kasa da kasa su ka bukata.

Abu Ridainah ya kara da cewa; An riga an kafa gwamnatin Falasdinu, kuma da akwai kasashe 149 da su ta amince da ita, kuma har ya zuwa yanzu ana samun Karin wasu kasashen da suke yin furuci da ita.

Kakakin kwarya-kwaryar  gwamnatin Falasdinawan ya yi ishara da yadda HKI da masu tafiyar da ita suke jefa duniya cikin rikici mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments