Guy Aviad: Kisan Jagororin Hamas Ba Zai Kawo Karshen Kungiyar Ba

Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da kashe Yahya Sinwar a jiya bayan wata arangama da aka yi da wasu mayakan Falastinawa ‘yan gwagwarmaya a yankin

Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da kashe Yahya Sinwar a jiya bayan wata arangama da aka yi da wasu mayakan Falastinawa ‘yan gwagwarmaya a yankin Rafah wanda  ta bayyana cewa Sinwar na daga cikin mayakan ad suka yi shahada a karawarsu da sojojin yahudawa.

Har yanzu dai babu wani bayania  hukuamnce daga bangaren Hamas da ke tabbatarwa ko kuma kore abin da Isra’iola ta fada da kuma hotunan da take ta yadawa.

Shugaban Amurka ya taya Firayi ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila murna kan kisan Sinwar, tare da bayyana hakana  matsayin wani babban ci gaba a abin da yakira yaki da ta’addanci

Wani bayahude mai sharhi kuma kwararre kan al’amuran Hamas, Guy Aviad, ya yarda cewa “Kungiyar Hamas za ta sake kafa karfinta tare da kwararrun mutane bayan kisan Sinwar da ma wasu jagororinta.”

Ya jaddada cewa “Sinwar babban jami’i ne, amma soja ne a wannan dogon yakin da aka yi tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, yakin da aka shafe shekaru da dama ana yi.”

Ya kara da cewa: Har yanzu akwai dubban masu fafutuka daga Hamas da sauran kungiyoyi a zirin Gaza.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channel 13 cewa: “Wadannan kungiyoyi suna karuwa kuma suna canzawa a kowane lokaci.

Da yake magana game da Hamas, ya kara da cewa: An gina mafi yawan karfin Hamas a lokacin da Sinwar yake tsarea  gidan kason Isra’ila, saboda haka koda babu Sinwar Hamas za ta ci gaba da wanzuwa kuma za ta kara karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments