Search
Close this search box.

Guterres ya ziyarci Ofishin Iran a MDD domin jajantawa kan shahadar shugaba Raisi

A yammacin jiya Juma’a ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci ofishin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Majalisar

A yammacin jiya Juma’a ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci ofishin dindindin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, domin jajantawa kan shahadar shugaba  Sayyid Ibrahim Raisi, da kuma Ministan Harkokin Waje, Hossein Amir Abdollahian.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci ofishin ne a  yammacin jiya Juma’a, inda ya yi ta’aziyyar shahadar shugaban kasar ta Iran, da ministan harkokin wajen kasar  da sauran wadanda suka rasa rayukansu tare da sua  hatsarin da ya auku.

Guterres ya yi wani rubutu da hannunsa a cikin wani littafi da ake yin rubutun ta’aziyya a ofishin Iran da hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya.

Bayan haka, babban magatakardar MDD ya yi wata gajeriyar ganawa da Amir Saeed Irani, jakadan kasar Iran a MDD.

A cikin ganawarsa da jakadan na Iran, Guterres ya bayyana alhininsa kan wannan lamari, tare da nuna juyayi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da kuma gwamnati da kuma al’ummar Iran baki daya.

A nasa bangaren jakadan na Iran ya yaba da yadda babban sakataren MDD ya nuna juyayi da alhininsa matuka dangane da abin da ya faru da manyan jami’an na kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments