Guterres Ya Gargadi Isra’ila Kan Hare-Harenta A Yankin Rafah Da Ke Gaza

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa, harin da Isra’ila ta kai kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza abu

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargadin cewa, harin da Isra’ila ta kai kan birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza abu ne da ba za a amince da shi ba.

Guterres ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella a ranar Litinin, inda ya ce: “Hare-haren Isra’ila kan yankin Rafah abu dab a za a taba amince da shi ba, domin zai haifar da matsalar  da za ta yi mummunan tasiri a kan yanayin da fararen hula suke ciki a yankin, da kuma kawo tarnaki ga ayyukan jin kai.”

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Hamas da su kara yin kokari don cimma matsaya.

Tun kafin wannan lokacin dai babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya sha yin kakkausar suka kan hare-haren Isra’ila a kan al’ummar Falastinu musamman ma a yankin zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments