Dubban jama’a ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga a gaban majalisar dokokin Birtaniya domin nuna goyon bayan Falasdinawa
Dubban daruruwan mutane ne suka fito zanga-zanga domin tunawa da cikan shekaru 76 da korar Falasdinawa daga muhallinsu da kuma nuna fushi da ci gaba da gudanar da bakar siyasar cin zarafin al’ummar Gaza tsawon watanni kusan takwas, kuma a cikin wadanda suka halarci zanga-zangar tare da yin jawabi har da Jeremy Corbyn, tsohon shugaban jam’iyyar Labour da kuma shahararren dan jaridar Falasdinu Moataz Aza’izeh.
Dubun dubatan jama’ar da suka fito zanga-zangar sun yi ta rera taken wajabcin ‘yancin kan al’ummar Falasdinu da komawar ‘yan gudun hijirar Falasdinawa kasarsu ta gado da kuma kawo karshen kisan kiyashin da ake wa Falasdinawa a Gaza gami da dage matakan killace yankin domin samun shigar da kayayyakin jin kai na bil’Adama.