Dubban yahudawan sahayoniyya sun gudanar da zanga-zangar neman ganin an cimma yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas
Dubban daruruwan yahudawan sahayoniyya ne suka gudanar da zanga-zanga a ranar Asabar a birnin Rehovot da ke tsakiyar yankunan Falasdinawa da aka mamaye, domin neman ganin gwamnatinsu ta kulla yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas tare da jaddada bukatar gudanar da zabe da wuri kafin lokacinsa domin kawo karshen gwamnatin fira minista Benjamin Netanyahu.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Dubban daruruwan yahudawan sahayoniyya ne suka taru a mahadar lambun kimiyya da ke birnin Rehovot domin neman yarjejeniyar musayar fursunoni da kuma gudanar da zabukan da wuri a haramtacciyar kasar Isra’ila.