Grossi da Gharibabadi  sun tattaun batun komawa shawarwari tsakanin Iran da IAEA

Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya ce ya yi tattaunawa mai ma’ana tare da Sakatare Janar na

Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) Rafael Grossi ya ce ya yi tattaunawa mai ma’ana tare da Sakatare Janar na Majalisar Koli ta Kare Hakkokin Dan Adam ta Iran Kazem Gharibabadi dangane da shirye-shiryen tafiyarsa zuwa Tehran.

Grossi ya fada a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa a shirye-shiryen ziyararsa mai zuwa a babban birnin Iran, ya gudanar da tattaunawa mai mahimmanci tare da Gharibabadi, wanda kuma ke rike da mukamin mataimakin ministan harkokin waje a bangaren shari’a da harkokin kasa da kasa.

Tun da farko Grossi ya ce a shirye ya ke ya tattauna da gwamnatin Iran ta 14 domin warware sauran batutuwan da suka shafi shirin Iran na nukiliya da ake Magana a kansu.

Bayan zaben shugaban kasa a Iran, na yi magana da shugaban Masoud Pezeshkian tare da bayyana niyyata  na ganawa da shi a Tehran don dawo da tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin hukumar IAEA da Iran,” in ji Grossi a taron kwamitin koli na IAEA na karshe da aka gudanar.

Har ila yau shugaban hukumar ta IAEA ya bayyana cewa, shugaban na Iran ya amince da ganawa da shi a lokacin da ya dace, yana mai bayyana fatan cewa za a gudanar da ganawar  nan ba da dadewa ba, kuma kafin zaben shugaban kasar Amurka.

Iran ta kara kaimi tun a shekarar 2019, bayan da tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da Washington daga yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, wadda aka fi sani da Joint Comprehensive Plan of Action (JCPOA), wadda aka rattaba hannu kanta a lokacin shugaba Barack Obama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments