Kungiyar ta Hizbullah tana cigaba da kai hare-haren mayar da martani akan HKI a cikin yankuna mabanbanta da suke karkashin mamaya.
Mayakan Hizbullah Sun Kai Hari a kan Barikin “Daud” na Haramtacciyar Kasar Isara’ila da can ne babbar shalkwatar sojan ‘yan mamayar a yankin Arewa.
A sanarwar da ta fitar bayan kai harin, kungiyar ta Hizbullah ta bayyana cewa; Saboda taimakawa al’ummarmu ta Falasdinu da suke jajurcewa a yankin Gaza, da kuma kare al’ummar Lebanon, kungiyar gwagwarmaya ta kai hare-hare a yau Laraba akan sansanin “Daud” ta hanyar harba gwamman makamai masu linzami.
Daga wannan sansanin ne dai sojojin HKI suke shiyar kai hare-hare a cikin Lebanon da kuma Syria.
Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta kai wasu hare-haren akan matsugunin ‘yan share wuri zauna na :Hatsur” ta hanyar harba gwamman makamai masu minzami.
A garin Safad kuwa makamai masu linzamin da kungiyar ta HIzbullah ta harba sun yi sanadiyyar tashin gobara a sassa daban-daban.
Kungiyar ta Hizbullah ta harba makami mai linzami samfurin “Ballistic” akan babbar shalkwatar kungiyar leken asiri ta Mosad daka Tel-Aviv”.