Gaza : Harin Isra’ila ya kashe mutane 20

Jiragen yakin Isra’ila sun kai wasu munannen hare-hare kan tantunan Falasdinawa a Khan Yunis, wanda hakan ya nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da saba

Jiragen yakin Isra’ila sun kai wasu munannen hare-hare kan tantunan Falasdinawa a Khan Yunis, wanda hakan ya nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da saba wa yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da kungiyar Hamas a watan Oktoban 2025.

Majiyoyin lafiya da na cikin gida sun ce jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare kan tantunan ‘yan gudun hijira a al-Mawasi, yammacin Khan Yunis, sau biyu cikin dan kankanin lokaci, inda suka kashe mutane akalla 20.

Jami’an lafiya sun ce 13 daga cikin wadanda suka mutu sun fito ne daga unguwannin al-Tuffah da al-Zeitoun na birnin Gaza.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai wani jariri dan wata daya.

Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce tun bayan tsagaita wuta, sojojin gwamnatin Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa 527 tare da raunata wasu 1,447.

Tun lokacin da Isra’ila ta fara kai hari kan Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023, hare-haren Isra’ila sun kashe Falasdinawa sama da 71,000 tare da raunata wasu sama da 171,000, yawancinsu mata da yara, yayin da suka lalata kusan kashi 90 cikin 100 na kayayyakin more rayuwa na Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments