Bayanai daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kai sabbin hare hare a a zirin Gaza da sanyin safiyar yau Asabar, wadanda sukayi sanadin shahadar fararen hula akalla 25 tare da jikkata wasu da dama.
A wayewar gari ne al’ummar Gaza suka farka da karar fashewar wasu bama-bamai daga sama da kasa na sojojin Isra’ila.
Rahotanni sun ce wani harin bam da aka kai a wani gida a unguwar al-Zaytoun da ke kudancin tsohon birnin Gaza ya yi sanadiyar mutuwar yara uku tare da jikkata wasu da dama.
An kuma kai hari wani gidan zama a kudancin garin Khan Younes. Inda aka bayar da rahoton shahada mutum hudu da jikkata wasu da dama.
A gabashin wannan birni, jiragen yakin gwamnatin Isra’ila sun kai hari wani gida a Absan al-Kabira, inda suka kashe fararen hula shida, ciki har da yara biyu, tare da jikkata wasu takwas.
Dama kafin hakan Sojojin Isra’ila sun kashe Karin Falasdinawa 12 a jerin hare-hare a yankin Gaza da aka mamaye, yayin da aka zakulo wasu gawawwaki daga wuraren da sojojin Isra’ila suka bari, da suka yi ka-ka-gida a wajen a baya.
Mai magana da yawun Cibiyar Kare Fararen Hula ta Falasdinawa Mahmoud Basal ya bayyana cewa an kashe Falasdinawa shida a wasu hare-haren Isra’ila biyu ta sama a Jabalia da ke arewacin Gaza, ciki har da wani hari da aka kai wa wani taron mutane.