Gaza: Mutane Suna Faduwa Akan Hanya Suna Mutuwa Saboda Yunwa

A wasu rahotanni da kungiyoyin kasa da kasa su ka fitar, sun bayyana cewa mutanen Gaza suna tafiya suna faduwa a sume, yayin da kananan

A wasu rahotanni da kungiyoyin kasa da kasa su ka fitar, sun bayyana cewa mutanen Gaza suna tafiya suna faduwa a sume, yayin da kananan yara suke mutuwa saboda yunwa.

Hukumar Agaji ta MDD a Gaza, “Unrwa” ta sanar da cewa; Faduwar mutane suna sumewa a yankin Gaza saboda yunwa wani yayani ne da ya zama ruwan dare.

Hukumar ta ce, mutanen suna faduwa ne a wuraren raba abinci, kuma babu karami, babu babba, ko mace balle namiji.

 Hukumar ta kuma yi kira da a bude iyakoki domin bayar da damar shigar da kayan abinci a cikin yankin na Gaza.

Har ila yau hukumar ta “Unruwa” ta ce; kananan yara sune wadanda su ka fi fuskantar mutuwa saboda yunwa, domin iyaye da dama ba za su iya ciyar da ‘yayansu ba.

Ita kuma hukumar lafiya ta duniya ta fitar da sanarwa da a ciki ta bayyana cewa a Gaza an mayar da yunwa ta zama makamin yaki wanda kuma  hakan yake haddasa mutuwar mutane da dama musamman kananan yara.

Sanarwar ta kuma ce; kaso 90% daga kananan yaran da shekarunsu suke kasa da shekaru 5, suna fama da rashin abinci mai gina jiki, kuma da dama daga cikinsu sun rasu saboda yunwa.

Hukumar ta “Unrwa” ta bayyana cewa; Yankin Gaza ya zama wuri mafi hatsari a doron kasa ga rayuwar kananan yara.

Har ila yau ta bayyana cewa; Baya ga rashin abinci a Gaza, magunguna ma sun kare a cikin asibitoci da cibiyoyin magani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments