Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana “matukar damuwarsa” kan keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ke yi akai-akai a zirin Gaza.
Da yake bayyana ga manema labarai a gefen taron koli na biyu na duniya kan ci gaban zamantakewa a Doha jiya Talata, Guterres ya ce: “Dole ne su dakatar da wadannan ayyuka, kuma dukkan bangarorin dole ne su mutunta sharuddan dake kunshe a matakin farko na yarjejeniyar zaman lafiya.”
“Muna aiki tukuru don kara taimakawa mutanen yankin Gaza; muna goyon bayan mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dawo da alaka tsakanin Gaza da Yammacin Kogin Jordan,” in ji Mista Guterres.
Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, hare-haren Isra’ila a Gaza na ci gaba da kashe Falasdinawa da dama kowace rana.
A makon da ya gabata, hare-haren Isra’ila a fadin Gaza sun kashe mutane sama da 100, ciki har da yara 46.
Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila na tsawon shekaru da dama kuma ya jaddada ‘yancin al’ummar Falasdinawa na neman ‘yancin kai.
Ya jaddada cewa, “Kada mu manta da bukatar kafa wata hanyar siyasa mai inganci don kawo karshen mamayar.”