Sojojin HKI sun kai falasdinawa 38 ga shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a yayinda wasu 203 suka je rauni a zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza na fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa tare da wadannan shahidan, adadin wadanda suka yi shahada tun ranar fara yakin tufanul Aksa, wato a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ya kai 45,097.
Ma’aikatar ta kara da cewa, wadanda suka ji rauni kuma, a cikin wannan lokacin sun kai 107,244.
Labarin ya kara da cewa a yau Laraba ce, ake cika kwanaki 439 da fara yakin, sannan a hare-haren su na karhe, jiragen yakin HKI sun yi ruwan boma-bomai kan asbitin Kamal Udwan da ke arewacin zirin gaza har sau 9.
Banda haka sun yi ruwan boma-bomai a kan wani gida a unguwar ‘Sahabai’ da ke birnin Gaza.
Sannan sun kai wadan nan hare-haren ne a dai-dai lokacinda aka fara tattaunawa don tsagaita wuta tsakaninsu da kungiyar Hamas a birnin Doha na kasar Qatar.
Sojojin HKI suna kai wadannan hare-hare ne, a dai-dai lokacinda ake tsananin sanyi, sannan ake karancin makamashi na dumama jiki. Musamman ga yara kanana masu shan nono, wadanda za su iya kamuwa da cututtuka daban-daban saboda sanyi.