Gaza: Qassam Sun Sanar Da  Sunayen Wasu Daga Cikin Kwamandojinsu Da Suka Yi Shahada

Dakarun rundunar “Izzuddin Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da sunayen wasu daga cikin kwamandojinsu da su ka yi shahada, gabani da kuma bayan tsagaita

Dakarun rundunar “Izzuddin Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da sunayen wasu daga cikin kwamandojinsu da su ka yi shahada, gabani da kuma bayan tsagaita wutar yaki.

Sanarwar wacce kungiyar ta Hamas ta fitar a yau Litinin a cikin faifan bidiyo, ta kunshi  sunayen Muhammad Sinwar ( Abu Ibrahim), wanda ya gaji shahid Muhammad Dhaif, ya zama babban kwamandan dakarun na Kassam.

Haka nan kuma Muhammad Shabanah, ( Abu Anas) da shi ne kwamandan rundunar Kassam a yankin Rafah, da ya yi shahada a tare da Muhammad Sinwar. Sai kuma Hakam Isa ( Abu Umar) wanda shi ma babban kwamanda ne na jihadi da ya yi ayyukan jihadi a kasashen Lebanon, Syria da wasu kasashe, kafin daga baya ya tare da Gaza.

Wani daga cikin kwamandojin da dakarun Kassam su ka sanar da shahadarsa, shi ne “Ra’id Sa’ad, ( Abu Mu’azu) da ya kasance a fagen kere-keren makamai.

Daga cikin shahidan da aka sanar da shahadarsu a yau Litinin din da akwai  Huzaifah Samir  Abdullahi al-kahlut ( Abu Ubaidah) da shi ne shugaban bangaren watsa labaru na rundunar ta Kassam, wanda kuma a tsawon lokacin yaki aka rika jin muryarsa yana yin sanarwa.

Dakarun na “Izzuddin-Kassam” sun ce al’ummar Falasdinu tana kare kanta ne, don haka babu yadda za a yi  su ajiye makamansu matukar ‘yan mamaya suna nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted