Gaza: Adadin Falastinawa da suka yi shahada ya haura 42,500

Rahotanni daga yankin zirin Gaza na cewa, akalla Falasdinawa 19 ne suka yi shahada  a harin Isra’ila a Gaza, wanda ya kai jimillar mutanen da

Rahotanni daga yankin zirin Gaza na cewa, akalla Falasdinawa 19 ne suka yi shahada  a harin Isra’ila a Gaza, wanda ya kai jimillar mutanen da aka kashe tun Oktoban bara zuwa mutum 42,519, cewar ma’aikatar lafiya ta yankin da ke ƙarƙashin mamaya.

Ma’aikatar ta ce wasu ƙarin mutane 99,637 sun samu raunuka sakamakon hare-haren da ke ci gaba.

“Dakarun Isra’ila sun kashe 19 sun kuma raunana mutum 91 cikin wani kisan kiyashi da suka yi wa wasu iyalai cikin awanni 24 da suka gabata,” cewar ma’aikatar.

“Wasu tarin mutane sun maƙale ƙarƙashin baraguzan gine-gine da kuma tituna, yayin da ma’aikatan ceto suka kas cim musu”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments