Fizishkiyan: Jinin Mutanen Da Aka Zubar Da Ba Su Ji Ba Su Gani Ba, Ba Zai Rabu Da Azzalumi Ba

Zababben shugaban kasar Iran Mas’ud PFzishkiyan ya wallafa wata kasida a shafinsa na “X da a ciki yake mayar wa da Fira ministan HKI martani,

Zababben shugaban kasar Iran Mas’ud PFzishkiyan ya wallafa wata kasida a shafinsa na “X da a ciki yake mayar wa da Fira ministan  HKI martani, inda ya ce, jinin mutanen da ba su ji ba su gani ba da aka zubar zai cigaba da bibiyar azzalumi ba zai rabu da shi ba.

 Fizishkiyan ya kuma cigaba da cewa; Babu yadda za a iya mancewa da laifukan kashe mutanen da ba su ji, ba su gani ba, haka nan kananan yara,balle kuma a girmama mai tafka laifi.

Shi dai Fira ministan HKI Benjemine Netenyahu ya kai ziyara Amurka inda ya gabatar da jawabi a gaban majalisar dokokin wannan kasa.

 Amurka ce kasar da ke kan gaba wajen taimakawa HKI da dukkanin abubuwan da take da bukatuwa da su, a yakin da take yi da al’ummar Falasdinu.

A can Amurka an rika gudanar da Zanga-zangar nuna kin amincewa da ziyarar da Netenyahu ya kai. Dama dai tun a watannin baya ne daliban jami’oin Amurka su ka rika yin gangami da gudanar da zanga-zanga nuna kin amince da yakin Gaza, suna masu yin kira da a kawo karshensa, sannan kuma a yanke taimakon da kasar tasu take bai wa Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments