Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun watsa labari a jiya, Litinin cewa: Fiye da jami’ai sojin yahudawan sahayoniyya 800 ne masu matsayi na Kanar da Laftanar Kanal suka mika takardar yin murabus dinsu daga aiki a wannan shekara ta 2024, a wani matakin da ba a taba gani ba.
Kafafen yada labaran yahudawan sahayoniyya sun tabbatar da cewa: A yammacin jiya litinin, wani soja ya halaka, yayin da wasu 10 suka samu raunuka sakamakon harin da ‘yan gwagwarmaya suka kai musu a Gaza.
Sannan shafin yanar gizo na yahudawan sahayoniyya mai suna “Isra’ila Ba tare da Cece-kuce ba” ya tabbatar da cewa: An kashe sojan Isra’ila daya sannan wasu 10 sun jikkata, ciki har da 3 da suke cikin mawuyacin hali, sakamakon fashewar wata nakiya da aka bisine a yakin Gaza. Yayin da wani jirgin saman sojin yahudawan sahayoniyya mai saukar ungulu ya fado a safiyar jiya Litinin a kan asibitin Soroka, da ya yi sanadiyyar jikkatan sojojin yahudawan sahayoniyya masu yawa da suke yaki a Gaza.
Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas, sun sanar da cewa: Sun kai hare-hare kan tankokin yaki guda biyu na Merkava da wata rundunar mamayar Isra’ila tare da bindige wani sojan yahudawa a yankin Shuja’iyya a Gaza.