Yemen: Firayi Ministan da wasu ministoci sun yi shahada a wani harin Isra’ila

Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta

Fadar shugaban kasar Yemen a Sana’a ta sanar da shahadar firayim minista Ahmed Ghaleb al-Rahwi tare da wasu ministocin kasar, sakamakon harin da Isra’ila ta kai a ranar Alhamis din da ta gabata.

Fadar shugaban kasar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta kara da cewa, wasu ministoci da dama sun samu raunuka sakamakon wannan ta’asa, kuma a halin yanzu suna samun kulawar lafiya.

Duk da haka, fadar shugaban kasar ta ba da tabbacin cewa cibiyoyi za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ga jama’a ba tare da wani tsaiko ba, duk kuwa da girman Rashin da aka yi.

Dangane da matsayar kasar Yemen kan batun yakin  Gaza, fadar shugaban kasar da ke  birnin San’a ta jaddada wa al’ummarta, da al’ummar Palastinu, da dukkan ‘yantattu na  al’ummar musulmi da al’ummomi duniya cewa, za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen nuna goyon baya ga al’ummar Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted