Firay Ministan Kasar Iraki Ya Ce Iran Da Amurka Suna Iya Samar Da Yarjeniyar Zaman Lafiya a Tsakaninsu

Firay ministan kasar Iraki Mohammad Shi’a Assudani ya bayyana cewa akwai matukar bukatar kasashen Amurka da Iran su cimma yarjeniya a tsakaninsu don ficewa daga

Firay ministan kasar Iraki Mohammad Shi’a Assudani ya bayyana cewa akwai matukar bukatar kasashen Amurka da Iran su cimma yarjeniya a tsakaninsu don ficewa daga yanayin zaman dar-dar da yankin yake ciki.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran IP ya nakalto Assudani yana fadar a haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa kasar Iran tana iya taka rawa na mai shiga tsakani idan akwai bukatar hakan don tabbatar da an kawar da halin da ake ciki a yankin.

 Har’ila yau jaridar Assharkul Ausat ta nakalto shi yana cewa yarjeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka zai yu.. Sannan da aka tambayeshi kan cewa gwamnatin kasar Iran tana da tasiri a kan gwamnatinsa, sai ya ce, babu inda Iran take sarrafa gwamnatin kasar Iraki. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Iraki kasa shen wacce take cin gashin kanta.

Daga karshe ya ce a iya saninta da JMI, babu wani alama da ke tabbatar da cewa Iran tana kokarin mallakar makaman nukliya.

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments