Fira Ministan Kasar Senegal Yana Ziyarar Aiki A Kasashen Yammacin Afirka

A ranar Alhamis da ta gabata ce Fira ministan kasar Senegal Usman Sonko ya bude ziyarar aiki a kasashen yamamcin Afirka domin kara dankon zumunci

A ranar Alhamis da ta gabata ce Fira ministan kasar Senegal Usman Sonko ya bude ziyarar aiki a kasashen yamamcin Afirka domin kara dankon zumunci da kasashen.

Daga cikin kasashen da ziyarar ta shafa dai akwai Cote-De Voire, Serra Lione, da Guinea Conakry .

A makon da ya gabata ne dai a yayin taron kira ga masu zuba hannun jari a kasar, senegak aka sanar da shirin ziyarar ta Fira ministan zuwa wadannan kasashe.

A Zangon farko na ziyarar a kasar Cote De Voire, fira ministan ya gana da Amadu Hot, wanda ya kasance dan takarar da Senegal ta tsayar, domin neman shugabancin Bankin Raya kasashen Afirka. Haka nan kuma ya gana da sabon shugaban Bankin na Raya kasashen Afirka, dan asalin kasar Mouritania Sidi Would Taha, ya kuma tattauna hanyoyin bunkasa dangantaka da bankin.

A kasar Guinea Conakri kuwa, fira minstan na Senegal ya gana da takwaransa  Amadu Bah, inda suka tattauna hanyoyin bunkasa dangantaka a tsakanin kasashensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments