Fira Ministan Kasar Lebanon Ya Bayyana Makircin ‘Yan Sahayoniyya Na Kai Hari Kan ‘Yan Jaridu

Fira ministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Lerbanin ya cewa: Hare-haren da gwamnatin mamaya ke kaiwa ‘yan jarida suna nufin tsoratar da kafafen yada labarai

Fira ministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Lerbanin ya cewa: Hare-haren da gwamnatin mamaya ke kaiwa ‘yan jarida suna nufin tsoratar da kafafen yada labarai ne

Fira ministan gwamnatin rikon kwarya ta kasar Lebanon Najib Mikati ya jaddada cewa: Sabon laifin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata na kai hari kan hedkwatar ‘yan jarida a birnin Hasbaiyya na kasar Lebanon, wani babi ne na laifukan yaki da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa, ba tare da fuskantar wata tsangwama ko kuma muryar kasa da kasa da zata iya dakatar da abin da ke faruwa ba.

Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya nakalto Mikati yana cewa: Hakika wannan harin da gangan ne da ke nufin tsoratar da kafafen yada labarai domin neman boye laifuka da barna da ake aikatawa, yana mai nuni da cewa an umurci ma’aikatar harkokin wajen kasar Lebanon da ‘yan kasashen waje da su hada wadannan sabbin laifuka a cikin jerin rahotonnin da ke rubuta laifukan haramtacciyar kasar Isra’ila da za a gabatar da su ga hukumomin kasa da kasa da suka dace, watakila hakan ya zaburar da duniya wajen hanzarta daukan matakan dakatar da wadannan cin zarafi da suke faruwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments