A jiya Laraba ne aka bude shari’ar tsohon madugun ‘yan tawayen kasar DRC Roger Lombala a kasar Faransa bisa tuhumar da ake yi masa da aikata laifuka akan bil’adama a yayin yakin DRC na biyu. Ana kuma tsammanin cewa wannan shari’ar za ta dauki wata daya ana yinta.
A yayin zaman shari’ar za a gabatar da shaidu daga wadanda su ka cutu sanadiyyar ayyukan kungiyar ‘yan tawayen wacce Lombala ya jagoranta.
Wannan shi ne karon farko da za a yi wa dan kasar DRC shari’a a kasar Faransa bisa ka’idar hurumin shari’a na duniya.
Ofishin Fada Da Laifuka Aka Bil’adama ( OCLCH) ya kama Lombala ne a ranar 29 ga watan Disamba 2020 a birnin Paris. An kuma gabatar da shi a gaban kotu a ranar 2 ga watan Janairu 2021 inda aka tuhume shi da; “Kitsa makirci da zummar aikata manyan laifuka akan bil’adama” da kuma ” Makarkashiyar aikata laifuka akan bil’adama.”
A cikin watan Nuwamba na 2023 aka tuhumi madugun ‘yan tawayen a karkashin wani tsari da doka da yake bai wa wata kasa yin shari’a akan laifuka masu hatsari da aka tafka, ba tare da la’akari da inda inda aka yi laifukan ba.
Ana zargin Lombala da kungiyarsa da cewa ya aikata laufukan a tsakanin watan Oktoba na 2002 zuwa watan janairu na 2003 a karkashin kungiyarsa ta “Gamayyar ‘yan Demokradiyya da Masu Kishin Congo” wacce kasar Uganda take taimakawa. A wancan tsakanin kungiyar ta yi kokarin shimfida ikonta a yankin Bini wanda yake cike da ma’adanai a gundumar Itori ta gabas. Daga cikin laifukan nasu da akwai kisa da kuma fyade da wawason dukiyar al’umma.