Falasdinawan Da Sukayi Hijira Sun Fara Komawa Arewacin Gaza

Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas

Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila.

Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi.

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza.

An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306, akasari mata da kananan yara.

Kungiyar Hamas dai ta ce gwamnatin Isra’ila ta amince da tsagaita bude wuta bayan da ta gaza cimma wasu manufofinta na yakin.

Tun da farko dai, gwamnatin kasar ta ce Falasdinawa za su iya komawa arewacin kasar a ranar Litinin bayan da kungiyar gwagwarmayar Jihadin Islama ta Gaza ta tabbatar da cewa za a saki dan Isra’ila Arbel Yehud kafin a yi musanyan fursunoni na gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments