Falasdinawa ‘Yan Gwagwarmaya Sun Gargadi Isr’ila Kan Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta

Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya sun gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza, tare da jaddada hakkinsu na

Falasdinawa ‘yan gwagwarmaya sun gargadi Haramtacciyar Kasar Isra’ila kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza, tare da jaddada hakkinsu na daukar matakin da ya kamata kan hakan.

Majiyar ta kara da cewa, bangarorin da ke shiga tsakani ma sun gargadi Isra’ila kan cewa,  ci gaba da keta wannan yarjejeniyar zai kawo babban cikas wajen aiwatar da ita.

Majiyoyin gwamnati a Gaza sun tabbatar da cewa, An samu keta yarjejeniyar sau da dama daga bangaren Haramtacciyar Kasar Isra’ila, ta hanyar yin amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare a kan fararen hula a cikin yankunan zirin Gaza, wanda hakan yake a matsayin babbar barazana ga ci gaba da wanzuwar wannan yarjejeniya, a cewar bayanin.

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa a Gaza, an isa da gawawwakin  shahidai fiye da 120 a asibitoci daban-daban tun bayan bayan sanar da dakatar da bude wuta, ciki har da gawarwaki 62 da aka tono  daga karkashin baraguzan gine-gine da Isra’ila ta rusa.

A halin da ake ciki, ma’aikatar lafiya a Gaza ta ba da rahoton jikkatar mutane 341 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sakamakon hare-haren Haramtacciyar Isra’ila a Gaza, lamarin da ke nuni da yanayi na rashin tabbas dangane da dorewar wannan yarjejeniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments