Falasdinawa Kimani  80,000 Ne Suke Halattar Salla A Masallacin Al-Aksa A Cikin Watan Ramadan

Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace, inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda

Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace, inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’i, wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shiga masallacin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin.

Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi.

Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin kansu, don fuskantar yahudawan Sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments