Rahotonni daga Gaza suna bayyana cewa: Adadin Falasdinawa da suka yi shahada a Zirin Gaza ya karu tun daga wayewar garin yau Juma’a zuwa shahidai 81 da suka hada da shahidai 42 a arewacin yankin, kamar yadda majiyoyin lafiya suka tabbatar, yayin da Falasdinawa 13 suka yi shahada, wasu kuma suka jikkata, a luguden bama-bamai da jiragen saman yakin sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a yankuna da dama na birnin Gaza.
Majiyar cikin gida a Gaza ta watsa rahoton cewa: Falasdinawa 9 ne suka yi shahada, yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin bam da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wasu tawagar Falasdinawa a shiyar arewacin sansanin ‘yan gudun hijira da ke gabar teku, arewa maso yammacin birnin Gaza.
Wasu Falasdinawa biyu kuma sun yi shahada, wasu kuma sun jikkata a wani farmaki da jiragen saman saki sojojin mamaya suka kaddamar a kusa da mahadar masana’antu a birnin Gaza.
Kamar yadda wasu Falasdinawa biyu suka yi shahada wani guda kuma ya jikkata sakamakon wani farmaki da jirgin saman yakin sojojin mamayar Isra’ila ya kai kan tashar ruwan masunta da ke yammacin birnin Gaza.