Falasdinawa 14 ne suka yi shahada a wani luguden wuta ta sama da sojojin mamayar Isra’ila ta yi kan yankuna da dama na Zirin Gaza
Sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a Zirin Gaza, a rana ta 458 a jere, ta hanyar kai hare-haren bama-bamai da dama ta sama da kuma harba makaman roka, a yayin da suke aiwatar da kisan kiyashi kan fararen hula, a daidai lokacin da ake cikin wani mummunan yanayi na jin kai sakamakon killace yankin da suka yi da kuma samun ‘yan gudun hijirar sama da kashi 95% na al’ummar yankin.
Shafin sadarwa na yanar gizo na Wafa ya bayyana cewa: A safiyar yau litinin Falasdinawa 14 ne suka yi shahada, sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka yi kan yankuna daban-daban na Zirin Gaza a rana ta 458 da fara yakin kisan kiyashi a yankin.
Majiyoyin cikin gida sun sanar da cewa jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai kan wani gida na iyalan Barakat da ke kusa da Birkat Sheikh Ridwan a arewacin birnin Gaza, inda suka kashe Falasdina hudu tare da raunata wasu na daban.