Falasdinawa 12 Ne Suka Yi Shahada A Harin Wuce Gona Da Irin Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza A Yau Laraba

Falasdinawa 12 ne suka yi shahada a Gaza yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankin

Falasdinawa 12 ne suka yi shahada a Gaza yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankin a yau

Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da zafafa matakan soji a zirin Gaza duk da kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na Isra’ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza.

Majiyoyin lafiya a asibitocin Gaza sun watsa rahoton cewa: Hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 12 da suka hada da hudu a birnin Gaza da bakwai a Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza, yayin da wani Bafalasdine daya ya yi shahada a yankin tsakiyar Falasdinu.

Jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wasu jerin hare-hare ta sama a kan wasu wuraren zama a birnin Gaza da tsakiyar da kuma kudancin zirin Gaza.

Majiyoyin cikin gida sun kuma bayar da rahoton cewa, sojojin mamayuar Isra’ila sun tayar da wata mota makare da bama-bamai a unguwar Al-Sabra da ke kudancin birnin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments